Nijer : Mahamadu Issufu Ya Yi Alkawalin Lashe Zabe Tun Zagayen Farko
A Ranar 21 Ga watan Fabrairu nan ne al'umma kasar ta Nijer ke kada kuri'a a zaben shugaban kasa gami dana 'yan majalisar dokoki
A Jamhuriya Nijer shugaban kasar mai barin gado Mahamadu Issufou ya yi alkawarin lashe zaben shugaban kasar dake tafe tun zagayen farko.
Mahamadu Issufu mai neman wa'adi na biyu a zaben shugabancin kasar ya bayana hakan ne a yayin taro shiga yakin neman zamen jam'iyyar sa ta PNDS tarraya.
koda yake dai za'a iya kallon wannan firicin nasa a matsayin farfagandan siyasa kasancewar ana cikin yakin neman zabe, aman a tarihin kasar dai babu wani dan siyasa daya taba lashe zaben shugaban kasa tun zagayen farko.
'Yan adawa dai a wannan kasar dake ganin hakan akan abunda bai zai taba yiwuwa ba, na zargin Mahamadu Issufu da rashin iya tafiyar da mulki, da cin hanci da rashawa daya mamaye mulkin sa dama jefa kasar cikin mastalar tsaro wannan kasar bata taba ganin irin sa ba.
Domin dai kalubalantar shugaba Mahamadu Isufu mai barin gado, mayan jam'iyyun adawa na kasar sun cimma matsaya guda na dafa ma wanin su daya fi samun kuri'u a zagayen farko.