Al'ummar Masar Sun Dawo Daga Rakiyar Shugabancin Abdul-Fatah Al-Sisi
Kuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka gudanar a kasar Masar tana nuni da cewa; Kashi 74 cikin dari na jama'ar da suka bayyana ra'ayinsu sun nuna rashin amincewarsu da ci gaba da shugabancin Abdul-Fatah Al-Sisi a kasar.
Shafin Nahrain net a yau Talata ya watsa sakamakon wata kuri'ar jin ra'ayin jama'ar Masar kan shugabancin Abdul-Fatah Al-Sisi da Cibiyar bincike kan harkokin sadarwa da ra'ayin jama'a a Masar ta gudanar a duk fadin kasar Masar, inda mafi yawan jama'ar da suka bayyana ra'ayinsu da suka kai kashi 74 suka nuna rashin amincewarsu da ci gaba da shugabancin Abdul-Afatah Al-Sisi.
Yayin da kashi 11 cikin dari suka bayyana gamsuwa da shugabancinsa, wasu kashi 15 cikin dari kuma suka bayyana rashin damuwarsu da yana yin yadda shugabancin kasar ke gudana a Masar.
Tabarbarewar harkar tattalin arziki da tsadar rayuwa gami da karin kudadaden haraji da na bukatun yau da kullum musamman wutan lantarki, ruwa da gas suna daga cikin manyan dalilan da suka sanya al'ummar Masar suka dawo daga rakiyar goyon bayan gwamnatin Al-Sisi.