Nijar : Lauyoyin Wadanda Ake Zargi Da Yunkurin Juyin Mulki Sun Kalubalanci Hukumomi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i10420-nijar_lauyoyin_wadanda_ake_zargi_da_yunkurin_juyin_mulki_sun_kalubalanci_hukumomi
A jamhuriyar Nijar lauyoyin mutanen nan da hukumomin kasar ke tsare da su bisa zarginsu da hannu a yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a cikin watan disamban bara, sun ce babu wata hujja da ke ba hukumomin kasar damar ci gaba da tsare mutanen a gidan kaso.
(last modified 2018-08-22T06:58:51+00:00 )
Sep 01, 2016 03:12 UTC
  • Nijar : Lauyoyin Wadanda Ake Zargi Da Yunkurin Juyin Mulki Sun Kalubalanci Hukumomi

A jamhuriyar Nijar lauyoyin mutanen nan da hukumomin kasar ke tsare da su bisa zarginsu da hannu a yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a cikin watan disamban bara, sun ce babu wata hujja da ke ba hukumomin kasar damar ci gaba da tsare mutanen a gidan kaso.

Kimanin mutane 24 ne ake ci gaba da tsarewa tun dai bayan da shugaban kasar Alh. Mahamadu Isufu ya sanar da yunkurin na yi masa juyin mulki a karshen watan Disamba shekara data gabata.

Saidai a cewar lauyoyin mutanen babu wasu hujjoji da har yanzu hukumomin kasar suke da su na ci gaba da tsare mutanen.

Mutanen da ake zargi dai sun hada da sojoji da kuma fararen hula galibi 'yan adawa.

A cewar Mal. Moussa daya daga cikin lauyoyin mutanen a wata hira da kanfanin dilnacin labarai na AFP kawai ana tsare da su ne bisa zargi ba tare da wata cikakkiiyar hujja ba.

A kwanan baya ne bangaren bincike na kotun soji a Yamai babban birnin kasar ya yi watsi da wata bukatar bada belin mutanen da ake zargi da hannu a kokarin yin juyin mulki wa gwamantin kasar a watan Disamba bara.

Idan ana tune, shugaban kasar ne Mahamadu Issufu ya sanar a shekara 2015 da ta gabata cewa jami'an leken asiri na kasar sun murkushe wani yunkurin juyin mulki wa gwamnatinsa.