Kasar Ghana Ta Koka Kan Jinkirin Bada Visa Ga Mahajjatan Kasar
(last modified Sat, 03 Sep 2016 12:56:16 GMT )
Sep 03, 2016 12:56 UTC
  • Kasar Ghana Ta Koka Kan Jinkirin Bada Visa Ga Mahajjatan Kasar

Hukumar Hajji da Umra na kasar Ghana ta koka kan yadda gwamnatin kasar saudia take jinkiri wajen bada Visar aikin hajji ga mahajjatan kasar na bana.

Shafin labarai na yanar gizo ya nakalto wani jami'in hukumar yana cewa a halin yanzu an fara umran tamattu'i amma har yanzu wasu mahajja 200 basu karbi Visarsu ba. Banda haka hukumar ta kara da cewa hukumon kasar ta saudia sun maida mutane 39 daga cikin mahajjan kasar don abinda suka kira karancin shekaru. 

Hukumar kasar saudia dai sun haka mutanen wasu kasashen musulmi da dama zuwa aikin hannin na bana, daga cikin su akwai kasar Iran, Yeman da Kuma Syria.