Zaben Jamhuriyar Nijar A Yau
A Yau Ne Al'ummar Nijer za su gudanar da zabe domin zaben sabon shugaban kasa da 'yan Majalisun dokokin kasar da za su jagoranci kasar tsahon shekaru biyar masu zuwa
Zaben na yau dai na cike da kalu bale, inda aka fuskanci kurakure da dama wajen shirya shi.a bangare guda kuma kasar na fuskantar barazanar ta'addanci na kungiyar Boko haram a kudu masu gabashin kasar.
'Yan takara 14 ne za su kara da shugaban kasar mai ci Alh Mahamadou Issoufu, inda da dama daga manazartan siyasar kasar ke ganin cewa a halin yanzu babu wani Dan takara da zai iya buga gaba ya ce shi zai Lashen na yau. saidai shugaban kasar tare da magoya bayansa na ganin cewa wankin hula ba zai kaisu dare ba, za su Lashe zaben tun a zagewa na farko saboda gagarimun aikin da suka ce sun yi da kuma yadda suka samu goyon bayan jam'iyu 43.
Saidai a bangare guda jam'iyun adawa na ganin cewa babu tantama su za su samu nasara a wannan zabe, saboda 'yan kasar suna bukatar canji, musaman ma a cewar su gwamnatin mai barin gado babu wani aiki da ta barkata bace jefa kasar cikin mawuyacin hali na kama karya da kuma cin hanci da rashuwa.
Manya-Manyan 'yan adawar da za su galubalanci shugaba Mahamadou Issoufou a zaben na yau sune Seyni Umar shugaban jam'iyar MNSD Nasara, Mahamane Ousmane Dan takarar jam'iyar MNRD Hankuri, da kuma Hamma Amadou shugaban jam'iyar Moderne F/A Lumana.
Kimanin 'yan Nijer Million 7 da dubu 500 ne aka sa ran za su kada kuri'unsu a yau domin zaben sabon shugaban kasa da 'yan Majalisun dokoki.