Wani Gungun Mayaka Ya yi Barazanar Kaiwa Nijar Hari
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i10735-wani_gungun_mayaka_ya_yi_barazanar_kaiwa_nijar_hari
Wani gungun mayaka dake kiran kansa mai fafatukar kwatowa kabilar tsirarun tubawa hakkinsu, ya yi barazanar kaiwa Nijar hari.
(last modified 2018-08-22T06:58:53+00:00 )
Sep 07, 2016 12:04 UTC
  • Wani Gungun Mayaka Ya yi Barazanar Kaiwa Nijar Hari

Wani gungun mayaka dake kiran kansa mai fafatukar kwatowa kabilar tsirarun tubawa hakkinsu, ya yi barazanar kaiwa Nijar hari.

A wata sanarwa da kanfanin dilnacin labaren AFP ya samu irinta gungun mai suna MJRN  ya ce yana shaidawa duniya anniyarsa ta yin amfani da makamai domin kwatowa al'ummar tubawa hakkinsu a Nijar.

Sanarwar da shugaban gungun na MJRN a takaice, Adam Tcheke Koudigan ya sa ma hannu, ta ce gwamnatin Nijar tayi kunnan uwar shegu da bukatun al'ummar tubawa duk da kiraye kirayen da sukayi tayi.

Gungun ya ce ya sha mika kukansa ga gwamnatin kasar akan yadda aka lalata wurarensu, duba da yadda kanfanonin ketare irinsu CNPC na China ke kwasar miliyoyin daloli ba tare da al'umma yankin sun samu komi ba, hasali ma lalata muhallansu.

A cikin faifan bidiyo dai da jagoran gungun Adam Tcheke Koudigan ya fitar an nuno jerin wasu kwarorin motoci samfarin komi da ruwan ka, inda yake cewa suna kan fagen daga idan lokaci yayi zasu iya kaiwa Nijar din hari koda yaushe.

Saidai a wata hira da kanfanin dilancin labaren AFP wani jami'in gwamnati da baiso a ambaci sunansa ba, ya shaida cewa shiri ne kawai na kafofin yada labarai, kuma shi Adam Tcheke Koudigan baida wasu magoya baya a kasar.