Gwamnatin Ghana Ta Hana Shigar Wasu Kayan Najeria A Cikin Kasar.
Mahukuntan kasar Ghana Sun sanar da Hana shiga da wasu kayayyakin Najeria cikin kasar.
Kafar watsa Labaran Afirka Time ta nakalto magabatan kasar na cewa ba wai kayan Najeria ba ne kawai aka hana shiga cikin kasar har da kayan wasu kasashen Afirka, kuma sun dauki wannan matakin ne domin karfafa tattalin Arzikin kasar, daga cikin ababen da aka hana shigar da su daga Najeria zuwa kasar ta Ghana a kwai Danyan Man fetur, siminti da kuwa magani.
Wannan mataki da mahukuntan kasar Ghanar su dauka na iya babbar illa ga tattalin arzikin kasar Najeria ganin cewa Ghana na daga cikin manyan kasashen dake da alakar kasuwanci mai karfi da Najeria a kasashen yammacin Afirka.
A cewar Ekwow Spio Garbrah ministan kasuwanci da masana'antun kasar Ta Ghana, daga yanzu kasar sa ta rage harakokin kasuwancin da ta ke yi tare da Najeria zuwa kashi 10% kacal.
A nasa waje, babban daraktan ma'aikatar wutar Ghana Kate Quartey-Papafio, wannan mataki da mahukuntar kasar suka dauka zai tilastawa mahukuntan Najeria tattauna da takwarorinsu na Ghana.