An kashe 'yan tawaye da dama a gabashin Kwango
Sojojin Demokradiyar Kwango sun sanar da kashe 'yan tawaye da dama a gabashin kasar
A wani bayyani da fitar a wannan Alkhamis,Dakarun tsaron Kasar Kwango sun sanar da kashe 'yan tawaye akalla 20 a yankin kivo ta arewa mai iyaka da kasar Ruwanda dake gabashin kasar.Rundunar ta ce ta kashe 'yan tawayen ne a wani sumame na musamman da ta kai musu, sannan kuma ta samu nasarar kame wasu 25 na daban bayan wadanda ta hallakan.
Wannan sanarwar na zuwa ne a yayin da Al'ummar kasar ke ci gaba da zanga-zangar gyamar Gwamnatin Joseph kabila, inda a jiya Laraba ma 'yan adawa suka gudanar da gagarumar zanga-zangar lumana inda suke zarkin Gwamnati da kuma Jami'ar tsaro da kasawa wajen tabbatar da tsaro da kuma kare rayukan fararen hula a kasar.
A makun da ya gabata ma, mazauna birnin Beni dake yankin Kivo ta arewa sun gudanar da zanga-zanga ta neman Gwamnati ta dauki matakin gaggauwa na kalubalantar hare-haren da 'yan tawaye ke kai masu a yankin.