Nijar : Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutane 38
A jamhuriya Nijar wasu sabbin alkaluma da ofishin kula da harkokin jin kai na MDD ya fitar sun nuna cewa, ya zuwa yanzu akalla mutane 38 ne suka rasa rayukansu kana wasu sama da 92,000 suka rasa gidajensu sakamakon bala'in ambaliyar ruwa da ta shafi wasu sassan kasar a 'yan watannin da suka wuce.
Ko baya ga hakan akwai wasu mutane 27 da suka ji rauni, an kuma samu hasara dabbobbi mayan da kananansu da yawan su ya kai 26,000, tare da lalata filayen noma eka 900 da kuma rushe gidaje sama da 9,000.
Rahoton da offishin hukumar ta OCHA reshen Yamai ya fitar ya ce matsalar ta fi shafar yankunan Agades da Tawa duk da cewa suna a yankin hamada, inda ba'a saba ganin irin hakan ba.
A cewar rahoton a wasu yankunan Agadas inda ba'a cika ma samun saukar ruwan sama ba, an samu sabkar ruwan har milimita 115 cikin awa guda, adadin da a cen baya ake samu a cikin shekara guda.