Tattaunawar Nijer da Libiya kan harakokin tsaro
Magabatan Kasashen Nijer da Libiya sun tattauwa a kan harakokin tsaro
Wata babbar tawaga na magabatan kasar Libiya bisa Jagorancin Shugaban Majalisar Dokokin kasar Aguila Saleh Isa ta ziyarci birnin Yammai fadar milkin kasar Nijer, a yayin wannan ziyara magabatan kasashen biyu sun tattauna kan batutuwan da suka shafi tsaro, musaman ma tsaron iyakokin kasashen biyu,tawagar ta gana da shugaban kasar Nijer Alhaji Mahamadu Issofou, a yayin ganawar ta su, shugaba Issoufou ya bukaci kasashen Duniya da su kafa runduna mai karfi wacce za ta kalubalanci 'yan ta'adda da'yan tawaye a kasar ta Libiya domin tabbatar da tsaro a kasar.
Magabatan Jumhoriyar Nijer nada akidar cewa shigar kasashen yamma da ya kawo karshen milkin marigayyi kanal Mu'amar Kaddafi a shekarar 2012, shi ne ya janyo tashin hankalin da kasar Libiya ke fuskanta.
Kasar Nijer dai na da iyaka da Libiyan da fadin ta ya kai kilomita 400.