Misrawa 16 sun rasu kafin fara aikin hajjin bana
Ministan Lafiya na Masar ya sanar da cewa ya zuwa yanzu Maniyata aiki hajji 'yan kasar 16 ne suka rasa rayukansu a Saudiya.
Ministan ya bayyana hakan ne bayan wani hadarin Mota da ya yi sanadiyar rasuwar Bamisire guda a kasar ta Saudiya.inda ya ce sauren Misrawa 15 din sun rasa rayukansu ne a dalilin rashin lafiya.
A nasa bangare Ministan tsare-tsare na kasar ta Masar Ashraf Al-Arabie da ke jagorantar mahajjatan na Masar ya ce A shekarar Bana Maniya aiki hajji na Kasar Dubu 62 da 511 ne za su sauke farari.
Bisa wani rahoto da Jaridar Al-Akhbar ta kasar Labnon ta watsa, bayan Jumhoriyar musulinci ta Iran, Masar ce kasa ta biyu ta tayi asarar yawan mahajatanta a shekarar da ta gabata sanadiyar turmutsutsun Mina.