Faransa ta bukaci kundin yarjejjeniyar tsagaita wuta a Siriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i11092-faransa_ta_bukaci_kundin_yarjejjeniyar_tsagaita_wuta_a_siriya
Kasar Faransa ta bukaci kundin yarjejjeniyar tsagaita wuta a Siriya
(last modified 2018-08-22T06:58:56+00:00 )
Sep 15, 2016 13:51 UTC
  • Faransa ta bukaci kundin yarjejjeniyar tsagaita wuta a Siriya

Kasar Faransa ta bukaci kundin yarjejjeniyar tsagaita wuta a Siriya

Jaridar Le figaro ta kasar Faransa ta nakalto Jean-Marc Ayrault Ministan harakokin wajen kasar Faransa a wannan alkhamis na cewa Faransa tana bukatar kundin yarjejjeniyar tsagaita wutar da aka cimma tsakanin magabatan kasashen Amurka da Rasha domin kadda a samu kuskure a kan hare-haren da ake kaiwa kan 'yan ta'adda a kasar.

Jean-Marc  ya kara da cewa shigar da Agajin gaggauwa zuwa kasar ta Siriya wata jarabawa ce na wannan yarjejjeniya.

A ranar Juma'ar da ta gabata ce kasashen Rasha da Amurka suka cimma yarjejjeniya tsagaita wuta na tsahon kwanaki 7 a kasar ta Siriya wacce ta fara aiki tun daga ranar Litinin da ta gabata wato ranar salla babba, saidai wannan yarjejjeniya ba ta shafi kungiyoyin 'yan ta'adda irin su IS ba,