An Kashe Mayakan Boko Haran A Kudu Maso gabashin Niger
An kashe mayakan kungiyar Boko Haram da dama a yankin Difa kudu maso gabcin Jumhuriyar Niger.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewa, wani harin ba zatan da sojojin kasar suka kaiwa mayaklan na Boko haran a wani wuri mai suna Tumur kilomita 75 daga arewacin Difa babban birnin yankin an kashe mayakan boko haram 30 sannan sojojin gwamnati 5 kuma suka rasa rayukansu. Sannan wasu sojojin gwamnati 6 suka ji rauni.
Garin Tumur dai yana kusa da takkin chadi kuma kan iyaka da tarayyar Nigeria. Kafin haka dai mayakan na Boko Haran sun kai hari a kan garin Boso a farkonwatan Yuni na wannan shekara inda suka kashe sojojin gwamnati 32 suka kuma raunata wasu da dama suka kuma karbi ikon garin na wani lokaci.
Harin na Boso dai shine hari mafi muni wanda mayakan Boko Haram suka kaiwa sojojin kasar tun watan Afrilun shekara da ta gabata.
Bayan haka ne gwamnatin kasar Chadi ta aike da dakarunta zuwa wannan yankin don haka irin wannan harin sake faruwa.