Gwamnatin Kasar Masar Ta Kara Tsananta Tsaro A Kan Iyakarta Da Libya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i11104-gwamnatin_kasar_masar_ta_kara_tsananta_tsaro_a_kan_iyakarta_da_libya
Sojojin Kasar Masar sun kara karfafa matakan tsaro a kan iyakar kasar da kasar Libya don hana mayakan yan ta'adda shiga kasarsu.
(last modified 2018-08-22T06:58:56+00:00 )
Sep 16, 2016 00:59 UTC
  • Shugaban Kasar Masar Abdulfata Sisi
    Shugaban Kasar Masar Abdulfata Sisi

Sojojin Kasar Masar sun kara karfafa matakan tsaro a kan iyakar kasar da kasar Libya don hana mayakan yan ta'adda shiga kasarsu.

Majiyar muryar Jumhuriyar Musulunci ta Iran ta nakalto wata majiyar sojojin kasar tana bayyana haka a jiya Alhamis ta kuma kara da cewa sojojin sun dauki wannan matakin ne bayan kashedin da ministan tsaron kasar faransa ya yi na cewa akwai yiyuwan yan ta'adda wadanda suke arcewa daga kasar Syria da Iraqi su shigo kasar Libya sannan su shiga kasashen Masar da kuma Tunisia daga can. 

Mahunkunta a kasar Masar dai sun yi kira ga kasashen duniya su tallafawa sojojin Halifa Haftar na kasar Libya don ganin a samar da rabbataccen zaman lafiya a kan iyakarta da Libya daga kudancin kasar.

A cikin makon da ya gabata ne sojojin Halifa Haftar suka sami nasarar  kwato wasu yankuna masu arzikin man fetur a gabacin kasar kan iyaka da kasar Masar.