Am Sami Yan Matsaloli A Zaben Jumhuriar Niger
Jam'iyyun adawa a zaben da aka gudanar a jumhuriyar Niger a jiya Lahadi sun bayyana cewa an sabi wasu matsalolin a zaben da aka gudanar a jiya lahadin.
Kamfanin dillancin labaran Chinhuwa na kasar China gamayyar jam'iyyun adawa a zaben shekara ta 2016 wacce ake kira COPA ta lisafta wasu matsalolin a zaben na jiya wadanda suka hada da jinkirin isowar kayakin zabe a rumfuna da dama a duk fadin kasar, rashi isassun katunan zabe a wasu rumfunan zabe, zabe fiye da sau guda a wasu wurare da kuma rashin shirya zaben kamar yadda ya dace a wasu wurare. Yan takarar shugaban kasa 15 ne suka yi takara a zaben zagaye na farko a jiya. Daga cikinsu har da shugaban kasa mai ci wato Mohammad Yusuf. Gamayyar Jam'iyyun adawar dai suna bukatar samin dan takara guda da zasu marawa a zagaye na biyu na zaben don kada Shugaban kasar mai ci.