Masar : An Bada Umurnin Rike Kaddarorin Masu Fafatuka
Kotu a Masar ta bada umurnin rike kaddarorin wasu shahararun masu fafatukar kare hakkin bil adama da kuma wasu kungiyoyi masu zamen kansu a ci gaba da bincike akan zubawa wata kungiyar fara hula kudi daga ketare.
Gwamnatin kasar dai ta ce ba zata taba amuncewa ba da duk wata kungiya da take samun tallafi daga ketare, ba tare da izininta ba.
Bangarorin da batun ya shafa sun hada da wasu shahararun masu fafatukar kare hakkin bil adama su guda biyar da kuma wasu kungiyoyi masu zamen kansu uku.
daga cikin mutanen da aka bada umurnin rike kandarorinsu da akwai Hossam Bahgat, dan jarida kana kan jagoran kungiyar EIPR mai fafatukar kare hakkin dan adam, sai kuma Gamal Eid shahararen kauya dake jagorantar wata kungiyar larabawa mai samar da bayyanai kan kare hakkin bil adama.
Tun a cikin shekara 2011 ne aka bude binciken bayan guguwar neman sauyi data yi awan gaba da mulkin tsohon shugaban kasar Hosni Moubarak.
Tuni dai kungiyoyin kare hakkin bil adama a ciki da wajen kasar irinsu Amnesty international suka kalubalanci wannan matakin da cewa na toye hakkin bil adama a kasar.