Sojojin Nijar Da Chadi Sun Kashe 'Yan Boko Haram 38 A Difa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i11179-sojojin_nijar_da_chadi_sun_kashe_'yan_boko_haram_38_a_difa
Hukumomin a Jamhuriya Nijar sun sanar da cewa dakarun kasar hadin gwiwa dana Chadi sun hallaka 'yan ta'addan Boko Haram 38 a yankin Difa dake kudu maso gabashin kasar.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Sep 17, 2016 13:35 UTC
  • Sojojin Nijar Da Chadi Sun Kashe 'Yan Boko Haram 38 A Difa

Hukumomin a Jamhuriya Nijar sun sanar da cewa dakarun kasar hadin gwiwa dana Chadi sun hallaka 'yan ta'addan Boko Haram 38 a yankin Difa dake kudu maso gabashin kasar.

Wannan dai na zuwa ne bayan hare haren da kungiyar Boko Haram ta kai a ranar Litinin a Toumour da kuma ranar Laraba a Gueskerou, dake yankin jihar Difa din mai iyaka da Najeriya.

Ayyukan tsarkake yankin da rundunar sojojin Nijar hadin gwiwa dana Chadi suka aiwatar sun taimaka wajen kashe 'yan ta'addan Boko Haram 38 da suka boye a yankin, inji wata sanarwar hukumomin Nijar a ranar Jumma'a a birnin Yamai.

Kakakin ma'aikatar tsaro kasar ta Nijar, Kanar Moustapha Ledru ya ce sojojin kasar sun kuma yi nasara kwace makamai masu yawa, da harsasai daga wajen 'yan ta'addan.