Nijar : An Sako Makusantan Hama Amadou
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i11221-nijar_an_sako_makusantan_hama_amadou
Babbar Jam'iyyar adawa ta MODEN Lumana a Jamhuriya Nijar ta tabbatar da sakin wadansu makusantan shugaban jam'iyyar su bakwai ciki har da Sumana Sanda wani tsohon ministan lafiya, bayan shafe wata 10 suna daure a gidan kaso.
(last modified 2018-08-22T06:58:57+00:00 )
Sep 18, 2016 23:25 UTC
  • Nijar : An Sako Makusantan Hama Amadou

Babbar Jam'iyyar adawa ta MODEN Lumana a Jamhuriya Nijar ta tabbatar da sakin wadansu makusantan shugaban jam'iyyar su bakwai ciki har da Sumana Sanda wani tsohon ministan lafiya, bayan shafe wata 10 suna daure a gidan kaso.

Wani mamba a jam'iyyar mai suna Seïni Mounkaila ya shaidawa manema labarai cewa an sallami Sumana Sanda shugaban jam'iyyar reshen Yamai da wasu jiga-jigan jam'iyyar su shida, bayan sun shafe watanni goma garkame a gidan yarin Say dake nisan kilomita kimanin 50 daga kudancin Yamai babban birnin kasar.

A ranar 12 ga watan Yuli ne wata kotu a Yamai ta yankewa mutanen hukuncin zamen gidan yari na watanni 10. 

Wadanda aka sakin dai makusanta ne ga tsohon shugaban majalisar dokokin kasar Hama Amadu wadanda aka zarga da tada -zaune- tsaye da kuma shirya tarurruka ba bisa ka'ida ba.

A ranar 14 ga watan Nuwamba na bara ne aka kama mutanen wadanda suka taru a filin sauka da tashin jiragen sama na Yamai don tarbar shugaban jam'iyyar Hama Amadou bayan dawowarsa daga Faransa inda yake gudun hijira.

Hama Amadu dai wanda ya zo na biyu a zaben shugaban kasar na watan Maris ya bar kasar ne saboda bita- da- kulin siyasar da ya ce ake masa akan badakalar nan ta safara jarirai.