Malaman Jami'an Nijar Sun Fara Wani Yajin Aiki Don Neman Hakkokinsu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i11248-malaman_jami'an_nijar_sun_fara_wani_yajin_aiki_don_neman_hakkokinsu
Malaman jami'oi a Jamhuriyar Nijar sun fara wani yajin aiki na mako guda don nuna rashin jin dadinsu da kin biyansu albashin da suke bin gwamnatin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:58:57+00:00 )
Sep 19, 2016 06:55 UTC
  • Malaman Jami'an Nijar Sun Fara Wani Yajin Aiki Don Neman Hakkokinsu

Malaman jami'oi a Jamhuriyar Nijar sun fara wani yajin aiki na mako guda don nuna rashin jin dadinsu da kin biyansu albashin da suke bin gwamnatin kasar.

Gidan radiyon France International ya jiyo wata majiya a Nijar din tana cewar a yau ne malaman jami'oin suka fara yajin aikin na su na mako guda, inda suka dakatar da duk wasu ayyuka na karantarwa da sauransu har sai an biya musu bukatunsu.

Rahotannin dai sun ce malaman jami'an suna bukatar gwamnatin ce da ta biya su kudaden da suke binta na watanni. Wannan dai shi ne karo na biyu da malaman jami'an suka gudanar da yajin aikin cikin 'yan kwanakin baya-bayan nan a kokarin da suke yi na kwato hakkokinsu daga hannun gwamnatin.

Ministan ilimi na Nijar din Muhammad Ben Omar ya ce gwamnati ta tattauna da malaman jami'an kan wannan batun, to amma matsalar tattalin arziki da ake fuskanta a kasar ita ce take haifar da matsaloli irin na rashin biyan malaman hakkokinsu.