Nuna Tsananin Damuwa Kan Aiwatar Da Kisan Kiyashi A Kasar Burundi
Sep 20, 2016 18:25 UTC
Tawagar bincike ta Majalisar Dinkin Duniya dake kasar Burundi ta nuna damuwarta kan yiyuwar aiwatar da kisan kiyashi a kasar.
Tawagar bincike ta Majalisar Dinkin Duniya da ke gudanar da aiki a kasar Burndi ta sanar da cewa: Gwamnatin kasar ita ke da alhakin matsalolin ci gaba da take hakkokin bil-Adama da suke faruwa a kasar, kuma akwai yiyuwar cin zarafin bil-Adama a kasar zai kai ga matakin aiwatar da kisan kiyashi.
Tawagar ta kara da cewa: Gwamnatin Burundi da msu goya bata baya suna daga cikin masu take hakkokin bil-Adama a kasar.
Tags