Murkushe Masu Zanga-zanga a kasar Habasha
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i1144-murkushe_masu_zanga_zanga_a_kasar_habasha
Kungiyar Kare Hakkin Bil-'adama ta "HUman Right Watch" ta yi Allah Wadai Da Murkushe Masu Zanga-zanga A Habasha.
(last modified 2018-08-22T11:27:51+00:00 )
Feb 22, 2016 19:24 UTC
  • Murkushe Masu Zanga-zanga a kasar Habasha

Kungiyar Kare Hakkin Bil-'adama ta "HUman Right Watch" ta yi Allah Wadai Da Murkushe Masu Zanga-zanga A Habasha.

Kamfanin Dillancin Labarun Faransa ya ambato wani jami'i na kungiyar kare hakkin bil'adaman ta "Humar Right Watch' da ke birnin Adis Ababa, yana cewa; Aikewa da jami'an tsaro masu yawa domin murkushe dalibai da manoma da sauran masu adawa da gwamnati, yana nuni ne da yadda gwamnatin ta ke kunnen uwar shegu da bukatun al'umma."

Kungiyar ta "Human Right Watch' ta kuma ce; kawo ya zuwa yanzu ba ta da cikakken bayani akan adadin mutanen da aka kashe ko kuma wadanda aka kama saboda rashin isa yankin Oromiya.

Kungiyar ta kuma yi kira ga gwamnati da ta kawo karshen amfani da karfin da 'yan sanda su ke yi da kuma sakin wadanda aka kama, sanann kuma a gudanr da bincike akan wadanda aka kashe.

Mazauna yankin Oromiya suna nuna adawarsu ne da shirin gwamnati na fadada babban birnin kasar Adis Ababa.