Congo : An Ci Zarafin Jama'a Gabannin Zabe
Wani rahoto da hadin gwiwar wasu kungiyoyin siyasa da na fararen hula suka fitar a kasar congo, ya nuna cewa akalla mutane dari ne aka ci zarafinsu gabanin zaben raba gardama da kuma na shugaban kasa da Denis Sassou Nguesso ya lashe.
Rahoton da bangarorin suka mikawa kwamitin kare hakkin bil adama na MDD, da kuma kotun hukuntan mayan laifuka ta duniya (ICC) ya kunshi bayanai daga makusantan wadanda lamarin ya shafa, da masu fafatuka, da jagororin jam'iyyun adawa da kuma wasu bayyanai daga gwamnatin kasar daya kama daga watan Satumban 2015 zuwa karshen watan Yuli wannan shekara ta 2016.
Daya daga cikin wadanda suka rubuta wannan rahoto ya shaidawa kanfanin dilancin labaren AFP cewa sunyi rejistan mutane sama da dari wadanda aka yanke masu hukunci ba tare da ma sun bayyana gaban shari'a ba, sannan akwai wadanda ake tsare da ba bisa doka ba, da kuma toye incin fadar albarkacin baki da kuma na 'yan jarida.
Makasudin fitar da wannan rahoto a cewar Mista Maurice Massengo-Tiassé shi ne neman a hukunta duk wani da yake da hannu a wannan aika-aika.