Nijer : An Fara Sanar Da Kwarya-Kwarya Sakamakon Zabe
Hukumar zaben kasar wato CENI na sa ran fitar da sakamakon zaben ne cikin kwanaki uku.
Hukumar zabe mai zamen kan ta a jamhuriya Nijer ta fara sanar da kwarya-kwarya sakamakon zaben shugaban kasa gami dana 'yan majalisun dokoki da aka kada a ranakun Lahadi da Litinin din nan.
Sakamakon da aka fara fitarwa a cikin daren jiyya Litinin ya hada dana kasashen waje dana wasu yankunan kasar, inda a cikin kasar shugaban Mahamadu Issufu ne mai barin gado ke kan gaba da kaso 35,66%, sai dan takara na Moden Lumana Hama Amadu mai bi mishi da 31,54 %, yayin da Seyni Omar na MNSD Nasara keda 10,57% ; sai tsohon shugaba Mahamane Ousmane, 6,38 %.
A Najeriya dai Jami’an zaben na Nijar a Abuja, sun ayyana dan takarar MODEN LUMANA, Hama Amadou kan gaba, sai Muhamadou Issoufou na PNDS TARAYYA, sai kuma Seyni Oumarou na MNSD NASSARA, A jihohin Rivers da Edo dai Jam'iyyar PNDS - tarraya ce ta lashe zaben, yayin da a kasar kamaru 'yan hamaya suka ce sun rungumi kadara.
Hukumar zaben kasar dai ta Nijer wato CENI na sa ran fitar da sakamakon zaben ne cikin kwanaki uku.