Masar Ta Bukci Hadin Kai Tsakanin Kasashen Iran, Saudiyya, Masar da Indonesiya
Sep 26, 2016 07:27 UTC
Ministan harkokin wajen kasar Masar ya bukaci hadin kai tsakanin kasashen Iran, Masar, Saudiyya da Indonesiya da nufin farfado da ci gaban kasashe masu tasowa.
A ganawarsa da jaridar Al-Yaumus-Sabi'i ta Masar: Ministan harkokin wajen kasar Samaha Shukri ya bayyana cewa: Samun hadin kai tsakanin kasashen Iran, Masar, Saudiyya da Indonesiya zai taimaka a fagen farfado da ci gaban kasashen masu tasowa.
Har ila yau Shukri ya jaddada matsayin kasarsa ta rashin amincewa da duk wani tsoma bakin kasashen waje a harkokin da suka shafi harkokin cikin gidan Masar.
Tags