Shugaba Kabila Ya Gana Da Paparoma Kan Rikicin Siyasar Kasr
(last modified Tue, 27 Sep 2016 05:51:34 GMT )
Sep 27, 2016 05:51 UTC
  • Shugaba Kabila Ya Gana Da Paparoma Kan Rikicin Siyasar Kasr

Shugaban kasar Demokradiyyar Kongo Joseph Kabila ya gana da shugaban mabiya darikar katolika ta duniya Paparoma Francis na 2 a fadarsa da ke Vatican na kasar Italiya don tattaunawa da shi dangane da rikicin siyasa da ya kunno kai a kasar.

A wata sanarwa da fadar ta Vatican ta fitar  ta bayyana cewar shugaban Kabila ya kawo wata ziyara  ta  kashin kansa fadar don ganawa da Paparoman inda suka tattaunawa kan batutuwa daban daban ciki kuwa  har da batun kalubalen da kasar take fuskanta biyo bayan rikicin siyasa da ya  kunno kai a kasar.

Sanarwar ta fadar Vatican har ila yau ta jaddada bukatar tattaunawa tsakanin 'yan siyasa da sauran kungiyoyin fararen hula na kasar don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar da kuma magance matsalolin da suka kunno kai cikin ruwan sanyi ba tare da tada hankula ba.

Kasar Demokradiyyar Kongon dai musamman babban birnin kasar, Kinshasa, ya shiga cikin wani yanayi na rikici da zanga-zangogi ne sakamakon gazawar da gwamnatin kasar  ta yi na tsayar da lokacin gudanar da zaben shugaban kasar don cike gurbin shugaba Kabilan wanda wa'adin aikinsa zai kare a karshen shekarar. 'Yan adawan dai suna zargin hukumar zaben kasar ne da kin gudanar da zaben da gangan don kara wa shugaba Kabilan wa'adin mulinsa.