Ci Gaba Da Cin Zarafin Fursunonin Siyasa A Gidajen Kurkukun Kasar Masar
A rahoton da kungiyoyin kare hakkin bil-Adama suka fitar a jiya Laraba yana dauke da bayanin cewa: Fursuononin siyasa suna ci gaba da fuskantar mawuyacin hali a gidajen kurkukun kasar Masar musamman gidan kurkukun Aqrab da ke birnin Alkahira fadar mulkin kasar.
Rahoton kungiyoyin kare hakkin na bil-Adama yana dauke da cewa: Jami'an tsaron gidan kurkukun Aqrab na birnin Alkahira suna daukan matakan musgunawa fursunonin da ake tsare da su a gidan kurkukun musamman fursunonin siyasa, inda suke daukan matakan duka da cin zarafinsu tare da cukusa tarin mutane masu yawa a cikin karamin daki mai kunci.
Rahotonnin da suke fitowa daga kasar ta Masar suna bayyana cewa: Matsalolin cin zarafin fursunoni tare da musguna musu kara tsananta suka yi a Masar idan aka kwatanta da baya kafin kifar da zababbiyar gwamnatin Muhammad Morsi na kungiyar Ihwanul-Muslimin. A wata kididdiga da cibiyoyin kare hakkin bil-Adama suka gudanar a Masar tana nuni da cewa: Bayan kifar da gwamnatin Muhammad Morsi a watan Yulin shekara ta 2013 yawan fursunonin da ake tsare da su a gidajen kurkukun Masar ba su wuce mutane 40,000 ba, amma tun bayan da Abdul-Fatah Al-Sisi ya dare kan karagar shugabancin kasar a matsayin farar hula a watan Yunin shekara ta 2014 zuwa yanzu, an samu karin yawaitan fursunonin da ake tsare da su a gidajen kurkukun kasar, kuma matsala mafi muni ita ce samun yawan mace-macen rayuka a gidajen kurkukun, inda ya zuwa yanzu aka kiyasta cewa: Fursuononin da suka rasa rayukansu sun haura mutane 140.
Kungiyoyin kare hakkin bil-Adama sun bayyana cewa: Mutuwar fursunoni a gidajen kurkukun Masar musamman fursunonin siyasa yana kara yawaita ne sakamakon rashin kayayyakin kiwon lafiya da matsalar cunkusa mutane fiye da kima a dakuna da suke kanana, baya ga dangogin azaba na jiki da na ruhi da fursunonin suke fuskanta.
Kafin zaban Abdul Fatah Al-Sisi a matsayin shugaban kasar Masar a karkashin tsarin dimokaradiyya ya dauki alkawarin kawo gagarumin canji a fagen rayuwar al'ummar Masar tare da wanzar da adalci ta hanyar mutunta hakkin bil-Adama, amma a cewar 'yan adawar kasar salon mulkinsa baya da bambanci da mulkin kama karya irin ta soji musamman a fagen murkushe 'yan adawar siyasa, karin bullar matsalolin take hakkokin bil-Adama da tsadar rayuwa da ta wurga al'ummar Masar cikin halin kaka-ni ka yi.
A gefe guda kuma a daidai lokacin da kungiyoyin kare hakkin bil-Adama suke kokawa kan matsalolin take hakkin dan-Adam a Masar, sai ga shi kasar ta Masar zata zame mamba a kwamitin kula da kare hakkin bil-Adama na Majalisar Dinkin Duniya daga shekara ta 2017 zuwa 2021 lamarin da manazarta kan harkokin siyasar kasa da kasa ke bayyana albarkacin bakunansu da cewa: Zabar kasar Masar a matsayin mamba a kwamitin kula da kare hakkin bil-Adama na Majalisar Dinkin Duniya al'amari ne da ke kara fayyace cewa babu wani tsayayyen tsari kan kare hakkokin bil-Adama a mahangar kungiyoyin kasa da kasa, kuma babu shakka wannan lamari yana matsayin kara karfafa mahukuntan Masar ne kan ci gaba da take hakkokin bil-Adama.