Nijar : Bakuwar Cuta Ta Kashe Mutane 25
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i11722-nijar_bakuwar_cuta_ta_kashe_mutane_25
Ma'aikatar lafiya a Jamhuriya Nijar ta sanar da cewa mutane 25 kawo yanzu suka rasa rayukansu sanadin kamuwa da bakuwar cutar nan ta zazzabi wace asalinta ta dabbobi ce amma takan iya kama mutane.
(last modified 2018-08-22T06:59:00+00:00 )
Sep 29, 2016 08:35 UTC
  • Nijar :  Bakuwar Cuta Ta Kashe Mutane 25

Ma'aikatar lafiya a Jamhuriya Nijar ta sanar da cewa mutane 25 kawo yanzu suka rasa rayukansu sanadin kamuwa da bakuwar cutar nan ta zazzabi wace asalinta ta dabbobi ce amma takan iya kama mutane.

Hakazalika akwai wasu mutane kimanin 73 da aka gano suna dauke da cutar kamar yadda  kakakin ma'aikatar kiwan lafiya na kasar Idrissa Maiga Mahamadou ya shaida a wani taron manema labarai.

Cutar dai mai suna (fièvre de la vallée du Rift) ta bulla ne a lardinan Tchintabaraden da Tassara dake jihar Tawa a tsakiyar kasar .

Tuni dai ma'aikatar kiwan lafiya kasar tayi gargadi ga jama'a da su takaita safara dabbobbi daga nan zuwa cen musamman daga yankin da cutar ta bulla zuwa inda babuta, kana a dinga tafasa madara da aka tatso daga dabbobin da suke da cutar kafin a sha.

Ana kuma iya kamuwa da cutar ta hanyar mu'amula da dabbobi ta ko wace hanya.

Wasu nau'in saboro ne mai suna (Aèdes da Culex)  ke yada cutar tsakanin dabbobi kana tana iya yaduwa zuwa ga mutane ta hanyar mu'amula da dabbobi da suka kamu da cutar.