Sojojin Nijar Da Chadi Sun Kashe 'Yan Boko Haram 123
Rundunar sojin Nijar ta ce dakarunta da hadin gwiwar na Chadi sun hallaka 'yan ta'addan Boko Haram 123, a ci gaba da samamen da suke kaiwa a yankin Diffa dake kudu maso gabashin kasar.
A cikin wata sanarwa, kakakin ma'aikatar tsaro ta Nijar, Kanar Moustapha Ledru ya ce sojoji ksar 14 sun rasa rayukansu kana wasu 29 sun samu raununaka a samamen da aka soma kaiwa tun farkon watan Yuli.
Kanar Ledru ya ce sojojin hadin gwiwar sun kuma kama wasu 'yan ta'adda biyu, tare da kwace makamai masu yawa, da harsasai daga wajen mayakan.
Kazalika a cewar Kanar Ledru, farmakin na hadin gwiwa da Chadi na tafiya a lokaci guda da wani hadin gwiwa na dakarun Nijar da Najeriya wanda shima ya bada nasara kwace mahimman yankuna daga hannun 'yan ta'addan a Najeriya da suka hada da Damasack, Abadan da Gachagar.
Sojojin sun kai samamen na hadin gwiwa ne a tsakanin ranar Litinin zuwa Laraba a kauyukan Gueskerou da Toumour, dake kudu maso gabashin Nijar.