Congo : Hukumar Zabe Na Son A Jinkirta Zabubuka
(last modified Sun, 02 Oct 2016 17:00:10 GMT )
Oct 02, 2016 17:00 UTC
  • Mista Corneille Naanga, shugaban hukumar zabe ta CENI a RD Congo
    Mista Corneille Naanga, shugaban hukumar zabe ta CENI a RD Congo

Hukumar zabe mai zamen kan ta a Jamhuriya demokuradiyyar Congo na son a jinkirta zabubukan kasar har zuwa watan Nowamba na shekara 2017 mai zuwa.

Matakin da ko kadan a cewar 'yan adawa na kasar bai gamsar dasu ba.

A ranar Asabar data gabata ce shugaban hukumar zaben kasar, Corneille Naanga, ya bayyana anniyar hukumar ta CENI na ganin an jinkirta zaben shugaban kasar gami dana 'yan majalisun dokoki dana wakilan kananan hukumomi.

Mista Naanga, na bayyana hakan ne a taron tattaunawa na kasar daya hada dukkan bangarorin al'umma kasar, da nufin samun mafita a rikicin siyasa da yaki- ci- yaki cinkewa a wannan kasa. 

Ana dai gudanar da taron tattaunawar na kasar tun farkon watan Satumba daya gabata, da nufin samun hadin kai da fahimtar juna akan jadawalin mayan zabubukan kasar da ake ta cacar baki a kai, tsakanin 'yan adawa da jam'iyya mai mulki musamen akan anniyar shugaba Joseph Kabila na sake tsayawa takara a zaben shugaban ksar duk da cewa kundin tsarin mulkin kasar ya haramta masa hakan.

Alkalumma dai sun nuna cewa kimanin mutane 49 ne suka mutu a zanga-zanga adawa da tazarcen shugaba J. Kabila  a ranakun 19 zuwa 20 na watan Satumba daya gabata.