'Yan Adawa Sun yi Watsi Da sakamon Zabe A Nijer
Yayin Da Hukumar Zabe Ci gaba da bayyana sakamakon Zabe a Jamhoriyar Nijer ,'Yan Adawa Sun Watsi da sakamakon farkon da aka fitar
Jam’iyyun adawa a Jamhuriyyar Nijar sun ce ba za su amince da sakamakon farko na zaben shugaban kasa ba inda shugaba Mahamadou Issoufou ke kan gaba a zaben.
‘Yan adawar sun bukaci magoya bayansu su yi watsi da sakamakon zaben.
Mai magana da yawaun ‘Yan adawar Amadou Babacar Cisse ya ce ba zasu amince da sakamakon da hukumar Zaben kasar CENI ta sanar ba.
‘Yan takara 14 ne suka fafata da Shugaba mai ci Mahamadou Issoufou na Jam’iyyar PNDS Tarayya kuma alamu na tabbatar da cewa shi zai lashe zaben tun a zagaye na farko.
An gudanar da zaben dai cikin kwanciyar hankali amma ‘Yan adawa sun soki hukumar zabe da gazawa musamman na rashin kai kayan zabe a wasu yankunan kasar da dama da suka jefa kuri’a a ranar Litinin.
'Yan Adawar Sun zarki mahukuntan kasar da Tilastawa hukumar zaben bayyana wasu alkaluma da basu da sahihanci, saidai hukumar zaben mai zaman kanta CENI ta yi watsi da wannan zarki.