An hallaka 'yan ta'adda 12 a tsibirin Sinai na kasar Masar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i11896-an_hallaka_'yan_ta'adda_12_a_tsibirin_sinai_na_kasar_masar
Majiyar tsaron Masar ta sanar da hallaka 'yan ta'adda 12 yayin wani gumurzu tsakanin Sojojin kasar da 'yan ta'addar a tsibirin Sinai
(last modified 2018-08-22T06:59:01+00:00 )
Oct 03, 2016 02:16 UTC
  • An hallaka 'yan ta'adda 12 a tsibirin Sinai na kasar Masar

Majiyar tsaron Masar ta sanar da hallaka 'yan ta'adda 12 yayin wani gumurzu tsakanin Sojojin kasar da 'yan ta'addar a tsibirin Sinai

Kamfanin dillancin Labaran Irna na kasar Iran ya nakalto majiyar tsaron Masar na cewa a yayin gumurzu da 'yan ta'adda Sojojin kasar sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda 12 a Hayyil-tarabin da kauyen Azzahir dake yankin Shekhi Zawid na arewacin tsibirin Sinai.har ila yau a jiya lahadin jami'an tsaron sun kai farmaki garin Al'arish, inda suka cabke mutane kimanin 200 da ake zarkin su da ta'addanci.

Rahoton ya ce kungiyar ta'addancin nan ta Ansaru Baitul Makdis ta fi ko wata kungiyar ta'addancin hadari a yankin Sinai, a cikin 'yan watanin da suka gabata kungiyar ta canza suna zuwa Wulayatu Sinai sannan kuma ta yi mubaya'a ga kungiyar IS.

Domin kalubalantar kungiyoyin 'yan ta'adda, Dakarun tsaron Masar din sun fadada kai hare-hare a tsibirin Sinai.