Yan Ta'adda Sun kashe Jami'an Tsaron Masar Biyar A Tsibirin Sina
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i11923-yan_ta'adda_sun_kashe_jami'an_tsaron_masar_biyar_a_tsibirin_sina
Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Masar ta sanar da cewa: Harin ta'addanci ya lashe rayukan 'yan sandan kasar biyar a garin Arisha da ke lardin Arewacin Tsibirin Sina.
(last modified 2018-08-22T06:59:01+00:00 )
Oct 03, 2016 13:50 UTC
  • Yan Ta'adda Sun kashe Jami'an Tsaron Masar Biyar A Tsibirin Sina

Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Masar ta sanar da cewa: Harin ta'addanci ya lashe rayukan 'yan sandan kasar biyar a garin Arisha da ke lardin Arewacin Tsibirin Sina.

Ma'aikatar harkokin cikin gidan Masar ta sanar da cewa: Wasu gungun 'yan ta'adda sun kai hari da makami mai linzami kan tawagar 'yan sandan Masar da suke gudanar da sintiri a garin Arisha a jiya Lahadi lamarin da janyo mutuwar 'yan sanda biyar.

Har ila yau wasu gungun 'yan ta'adda sun kai harin kwanton bauna kan tawagar 'yan sandan Masar a garin na Arisha a ranar Asabar da ta gabata, inda harin ya yi sanadiyyar mutuwar 'yan sanda uku.

A cikin 'yan kwanakin nan ana samun bullar dauki ba dadi tsakanin jami'an tsaron Masar da gungun 'yan ta'adda a yankunan da suke lardin Tsibirin Sina duk da matakan da jami'an tsaron kasar suke dauka na zafafa kai hare-hare ta sama da kasa kan 'yan ta'addan.