'Yan Sandan Masar Sun Bindige Wani Babban Kusa A Kungiyar Muslim Brotherhood
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i11944-'yan_sandan_masar_sun_bindige_wani_babban_kusa_a_kungiyar_muslim_brotherhood
'Yan sandan kasar Masar sun bindige wani babban kusa na kungiyar Muslim Brotherhood da aka haramta a kasar tare da wani memba a kungiyar har lahira yayin wani musayen wuta tsakanin bangarori biyu a daren jiya.
(last modified 2018-08-22T06:59:01+00:00 )
Oct 04, 2016 07:46 UTC
  • 'Yan Sandan Masar Sun Bindige Wani Babban Kusa A Kungiyar Muslim Brotherhood

'Yan sandan kasar Masar sun bindige wani babban kusa na kungiyar Muslim Brotherhood da aka haramta a kasar tare da wani memba a kungiyar har lahira yayin wani musayen wuta tsakanin bangarori biyu a daren jiya.

A cikin wata sanarwa da ma'aikatar cikin gidan kasar  ta fitar ta ce 'yan sandan sun bindige Muhammad Kamal dan shekaru 61 da kuma Yasser Shehata Ali Ragab wanda shi ma dan kungiyar Muslim Brotherhood din ne a lokacin da 'yan sandan suka kai samame inda suke boye a Kudu maso gabashin birnin Alkahira a jiya Litinin a kokarin da ake yi na kama su.

Sanarwar ta kara da cewa 'yan sandan dai sun jima suna neman Muhammad Kamal din, wanda likita ne, saboda zargin da suke masa da hannu cikin wasu hare-hare da ake zargin 'yan kungiyar sun kai. A baya ma an taba yanke masa hukuncin zaman gidan yari na rai da rai har sau biyu a bayan idonsa. Har ila yau sanarwar ta ce ya kasance yana jagorantan bangarori daban-daban masu dauke da makami na kungiyar.

Shi ma Yasser Rajab din da aka kashe su tare an taba yanke masa  hukuncin zaman gidan yari na shekaru 10.

Sai dai ita kuma kungiyar ta Muslim Brotherhood, cikin wata sanarwa da ta buga a shafinta, ta ce tana da  tabbacin cewa Mr, Kamal yana hannun 'yan sandan bayan sun kama shi don haka za su dora alhakin duk wani abin da ya same shi a kan gwamnatin Masar din.