Burundi Ta yi Watsi Da Kafa Kwamitin Bincike Na Majalisar Dinkin Duniya
Brundi ba ta amince da kwamitin bincike na majalisar dinkin duniya ba.
Gwamnatin Burundi ta nuna kin amincewa da kafa kwamitin bincike na majalisar dinkin duniya akan rikicin kasar.
Kamfanin Dillancin Labarun Reuters ya ambato majiyar gwamnatin ta Burundi tana cewa; Tunanin kafa kwamitin bincike akan rikicin da kasar ta ke fuskanta na siyasa, wani tunani ne na gefe daya ba tare da cikakkiyar masaniya akan gaskiyar lamari ba.
Kwamitin kare hakkin bil'adama na majalisar dinkin duniya ya amince da kafa kwamitin bincike, a ranar juma'a domin aika shi zuwa kasar Burundi. Kwamitin kare hakkin bil'adama na majalisar dinkin duniyar ya kara da cewa;An amince da kafa kwamitin ne bayan rahoto da kwamitin bincike da ke nuni da tabbatar da take hakkin bil'adama.
Tazarcen da shugaba Pierre Nkurunziza ya yi a 2015 ne ya jefa kasar Burundi cikin rikicin siyasa.