Halakar 'Yan Ta'adda A Yankin Tsibirin Sina Na Kasar Masar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i11995-halakar_'yan_ta'adda_a_yankin_tsibirin_sina_na_kasar_masar
Jami'an tsaron Masar sun kashe wasu gungun 'yan ta'addan kungiyar Baitu-Maqdis a yankin Tsibirin Sina na kasar.
(last modified 2018-08-22T06:59:02+00:00 )
Oct 05, 2016 02:19 UTC
  • Halakar 'Yan Ta'adda A Yankin Tsibirin Sina Na Kasar Masar

Jami'an tsaron Masar sun kashe wasu gungun 'yan ta'addan kungiyar Baitu-Maqdis a yankin Tsibirin Sina na kasar.

Majiyar tsaron Masar a jiya Talata ta sanar da cewa: Jami'an tsaron sun kashe wasu gungun 'yan ta'adda ta mutane takwas mambobin kungiyar ta'addanci ta Baitu-Maqdis a wani dauki ba dadin da suka yi a lardin Arewacin Tsibirin Sina na kasar.

Majiyar 'yan sandan Masar ta sanar da cewa: Gungun 'yan ta'addan na mutane takwas su ake zargi da hannu a datse kan wasu matasa biyu a wani kauye a yankin Tsibirin na Sina kwana guda kafin halakarsu.

A gefe guda kuma ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Masar ta sanar da cewa; Jami'an tsaron kasar sun kashe wasu 'yan ta'adda biyu Muhammad Kamil da Yasir Shahata a musayar wutan da suka yi a tsakaninsu. Muhammad Kamil dai tsohon mamba ne a ofishin gudanarwa na kungiyar Ihwanul-Muslimin, kuma kotu ta yanke masa hukuncin dauri rai da rai a gidan kurkuku duk da cewa ba a kai ga makama shi ba.