Tawagar Tarayyar Afirka Za Ta Ziyarci Kasar Burundi
(last modified Wed, 24 Feb 2016 09:23:54 GMT )
Feb 24, 2016 09:23 UTC
  • Tawagar Tarayyar Afirka Za Ta Ziyarci Kasar Burundi

Kungiyar Tarayyar Afirka Za ta Aike Da Tawaga Zuwa Kasar Burundi

Kamfanin Dillancin Labarun Faransa daga birnin Johannesburg ya ambato fadar shugaban kasar Afirka ta kudu tana cewa; kungiyar tarayyar afirka tana shirin aikewa da tawaga zuwa kasar Burundi a ranakun 25 da 26 na watan nan na Febrairu da ake ciki.

Shugaban kasar Afirka ta kudu Jacob Zuma wanda sanarwar ta fito daga ofishinsa ya kara da cewa; tawagar za ta kunshi shugabannin kasashe da kuma pira ministoci na kasashen da su ke mambobi a kungiyar ta tarayyar afirka da su ka hada da Senegal da Murtaniya da Gabon da Habasha.

A cikin watan Janairu da ya shude ne dai tarayyar afirkan ta janye shirinta na aikewa da dakarun tabbatar da zaman lafiya zuwa kasar Burundi bayan da kasar ta ki bada hadin kai.