Jamus za ta kafa sansanin Soja a Nijer
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i12094-jamus_za_ta_kafa_sansanin_soja_a_nijer
Kasar Jamus ta bayyana shirin ta na kafa Sansanin Soja a Jumhoriyar Nijer
(last modified 2018-08-22T06:59:02+00:00 )
Oct 07, 2016 01:35 UTC
  • Jamus za ta kafa sansanin Soja a Nijer

Kasar Jamus ta bayyana shirin ta na kafa Sansanin Soja a Jumhoriyar Nijer

Maku guda bayan da kasar Amurka ta sanar da kafa Sansanin Soja a Nijer, Jakadar Kasar Jamus a Nijer shima ya sanar da shirin kasar na kafa Sansanin Soja da zai  taimakawa Dakarun dake yakar masu da'awar Jihadi a kasar Mali.

Jakadar ya kara da cewa Jamus a shirye take ta bayar da babbar gudumuwa a yankin sahara na kasashen Afirka, sannan ya bayyana Nijer din a matsayin babbar abokiya a fagen yaki da ta'addanci da kuma bakin haure.

A karshen watan Satumbar da ya gabata ne Gwamnatin kasar Amurka ta tabbatar da gina wani sabon Sansanin Soja da zai lakume miliyan 50 zuwa 100 na $ a jihar Agadez dake arewacin kasar ta Nijer.

kafin hakan dai, Kasar Amurka na da Sansanin Sojan sama a birnin Yamai fadar milkin kasar, inda daga can ne take taimakawa Sojojin MDD dake yaki da ta'addanci a kasar Mali kalkashin jagorancin kasar Faransa, da kuma Sojojin kasashen Murtaniya, Burkina Faso, Tchadi da ita kan ta Nijer din a fagen yaki da ta'addanci.

A wannan lahadi ne ake sa ran shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel za ta fara ziyarar aiki na kwanaki uku a  kasashen  Habasha , Nijer da Mali dan tattaunawa da shugabanni da kasashensu ke zama hanyoyi da bakin haure ke bi a kokarin su  na zuwa  kasashen Turai