Mutane da dama sun rasu sanadiyar wani sabon rikici a Tsakiyar Afirka
Mata majiya mai alaka da MDD ta sanar da mutuwar Mutane da dama sanadiyar billar wani sabon rikici a kasar Afirka ta tsakiya.
Kafar watsa labaran Annashra ta kasar Labnon ta nakalto Shugaban sadarwa na Dakarun MDD dake kasar Afirka ta tsakiya na cewa rikicin da ya faru a ranar Talatar da ta gabata ya yi sanadiyar mutuwar mutane 11 tare kuma da bacewar wasu 11 na daban yayin da wasu 14 suka jikkata.
Jami'in ya ce rikicin ya kunno kai ne bayan da wani gungun 'yan bindiga sun hallaka wani babban jami'in Soja a birnin Bangui, kuma a halin da ake ciki komai ya lafa.
A ranaikun Talata da Larabar da suka gabata Dakarun MDD suka fara kai dauki domin kare lafiya fararen hula da kuma kontar da tarzoma a wuraren da rikici ya kunno kai. MDD da magabatan kasar sun bukaci Al'umma da su mayar da martani a duk lokacin da aka kai musu hari.
Rahoton ya ce bayan kisan gillar da aka yiwa babban jami'in Sojan, kungiyoyin dake dauke da makamai a yankuna daban daban na cikin kasar sun fara masayar wuta a tsakanin su, domin kontar da tarzoma, Dakarun tsaron na Majalisar Dinkin Duniya sun kai dauki a duk wuraren da rikicin ya barke.