Shugabar Gwamnatin Jamus Za Ta Ziyarci Nijar
A wannan Litinin ce shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, ke fara wata ziyara aiki a Jamhuriya Nijar a ci gaba da ran gadin da take a wasu kasashen nahiyar Afrika.
A yayin ziyara ta yini guda, Madame Merkel za ta gana da shugaban kasar ta Nijar Alhaji Mahamadu Isufu, kan batutuwan da suka shafa alakar dake tsakanin kasashen biyu da batun bakin haure da kuma tsaro.
Kasashen Nijar da Jamus nada alaka ta kusan shekaru 55, kuma wannan dama ce tsakaninsu a cewar hukumomin Nijar na yin waiwaye akan yadda huldar ke tafiya tsawan wadanan shekaru.
kafin jamhuriya Nijar dai shugabar gwamnatin ta Jamus ta ziyarci kasar Mali, kuma bayan Nijar zata isa kasar Habasha.
Ana sa ran bayan wannan ran gadin Angela Merkel zata gana da shugabannin kasashen Najeriya da Chadi a birnin Berlin na kasar Jamus.