Ficewar bazata na Jakadan kasar Saudiya daga birnin Alkahirar Masar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i12403-ficewar_bazata_na_jakadan_kasar_saudiya_daga_birnin_alkahirar_masar
Jakadan Saudiya a kasar Masar ya fice daga cikin kasar
(last modified 2018-08-22T06:59:04+00:00 )
Oct 13, 2016 07:42 UTC
  • Ficewar bazata na Jakadan kasar Saudiya daga birnin Alkahirar Masar

Jakadan Saudiya a kasar Masar ya fice daga cikin kasar

A ranar Larabar da ta gabata Jakadan kasar Saudiya dake birnin Alkahirar Masar  Ahmad bn Abdul-aziz Katan ya yi ficewar bazata daga birnin na Alkahir, wasu majiyoyin na cewa rashin jutuwar da ta kunno kai a 'yan kwanakin nan tsakanin kasashen biyu shi ne musababin da masarautar Ali sa'oud ta kira jakadan na ta na birnin Alkahira.

Wasu Majiyoyin na ganin cewa dakatar da taimakon Man fetur da kasar Saudiyan ke baiwa kasar Masar da kuma kuri'ar da Masar ta kada na goyon bayan kasar Rasha kan rikicin Siriya na daga cikin dalilan da suka janyo rashin jituwa tsakanin kasashen biyu.ganin cewa magabatan na Saudiya ba su taba tunanin hakan ba daga kasar Masar shi ya sanya magabatan na Saudiya suka yi takaici dangane da matsayar magabatan Masar din dangane da kasar Siriya

kafin hakan dai,Kamfanin Man fetur Aramco na kasar saudiya  ya ce ya dakatar da duk wata mu'amala da yake yi tare da kasar Masar ba tare da bayyana wani dalili ba.sannan kuma kasar ta Saudiya ta rufe ofishin tashar Al-arabiya kafin daga bisani Jakadar Saudiyar ya fice daga birnin Alkahirar a jiya Laraba