Taron kai harin gare dangi a kan Kungiyar Boko haram
Manyan komondojin yankin tabkin Chadi sun fara gudanar da taro domin duba hanyoyin da ya kamata su bi wajen kai harin kare dangi kan kungiyar boko haram a Jumhoriyar Nijer
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta cewa A jiya Alkhamis Manyan komondojin kasashen Najeriya, Nijer , Chadi, Kamaru da kuma Benin sun fara gudanar da taro da nufin bincike kan hanyoyin kai hari kare danki kan kungiyar Boko haram a birnin Yamai na jumhoriyar Nijer.
A yayin buda taron, Ministan tsaron Nijer Hassoumi Massoudou ya bayyana cewa daga watan yunin da ya gabata zuwa yanzu kasashen Nijer, Chadi da Najeriya sun gudanar da aiyukan leken asiri da dama kan sansanonin kungiyar Boko haram kuma shakka babu wani aiki ya bada sakamako mai kyau wajen kai hari kan 'yan ta'addar.
Ministan ya kara da cewa hare-haren da Dakarun tsaron kasashen Chadi, Nijer da Najeriya ke kaiwa kan 'yan ta'addar na boko haram ya yi sanadiyar 'yanto yankuna da dama dake hanun 'yan boko haram din a baya.