MDD Ta Yanke Shawarar Aike Da Sabom Jakada Zuwa Kasar Burundu
(last modified Sun, 16 Oct 2016 05:44:09 GMT )
Oct 16, 2016 05:44 UTC
  • MDD Ta Yanke Shawarar Aike Da Sabom Jakada Zuwa Kasar Burundu

Majiyar majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa majalisar zata aike da sabon jakada zuwa kasar Burundi a kokarinta na dawo da zaman lafiya a kasar.

Majiyar muryar Jumhuriyar musulunci ta Iran daga birnin NewYork ta bayyana haka ne a wannan makon da muke ciki ta kuma kara da cewa Jamal bin Umar ne majalisar zata aika zuwa birnin Bujumbura babbabn birnin kasar ta Burundi. Kuma zai kama aiki gadan gadan a cikin mako mai kamwa . 

A baya bayan nan dai gwamnatin kasar ta Burundu ta yi barazanar ficewa daga koton kasa da kasa idan majalisar ta ci gaba da takura mata. Shugaban kasar ta Burundi Pierre Nkruziza yayi wannan barazanar ce a lokacinda majalisar ta kuduri anniyar aike da jami'an tsaro zuwa kasar don tabbatar da zaman lafiya a kasar amma ya ki amince da hakan. Bisa binciken da kungiyoyin kare hakkin bil'adama daban daban suka yi, jami'an tsaron kasar na Burundi wanda ya hada da sojoji da kuma yansanda suna da hannu dumu dumu wajen kashe fararen hula a rikicin siyasar kasar wanda aka fara tun shekara ta 2015 da ta gabata. 

Tun bayan zaben shugaban kasa wanda aka gudanar a cikin watan yulin shekarar da ta gabata ne kasar Burundi ta fada cikin matsalolin siyada wadanda suka cinye rayuka muntane kimani 500 ya zuwa yanzu sannan wasu dubban kuma suka bar kasar don tsira da ransu.

Jam'iyyun adawar kasar ta Burundi sun bayyana cewa shugaba Pier Nkruziza ya tsaya zaben shugaban kasa a karo na ukku ne wanda kundin tsarin mulkin kasar bata amince da hakan ba. don haka suka bukace shi da ya sauka kan kujerara shugabancin kasar. Ko kuma a gudanar da zabe mai inganci.

A cikin watan Jenerun shekarara da muke ciki ne komitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya fitar da wani kuduri mai lamba 228 na aikewa da jami'an yansanda na kasa da kasa zuwa birnin Bujumbura da kuma wasu yankunan kasar don kawo karshen zubar da jini da ke faruwa a kasar, amma gwamnatin kasar ta Burundin ta kesasa kasa ta ki amincewa da kudurin ta ki kuma barin yansandanm su shiga kasarsa. 

Sannan kafin haka ma kungiyar tarayyar Africa AU ma ta yi yunkurin aikewa da rundunar tabbatar da zaman lafiya zuwa kasar ta Burundin amma gwamnatin kasar ta hana hakan faruwa.

Jakadan kasar Faransa a komitin tsaro na majalisar dinkin duniya Idan Francois Delattre ya bayyana cewa idan kasar Burundi ta yi watsi da kudurin na MDD akwai wasu hanyoyi wadanda majalisar zata bi don tilasta mata amincewa da ita, Francois ya kara da cewa hanyoyin sun hada da dorawa manya manyan jami'an gwamnatin kasar takunkuman tattalin arziki da kuma hana a sayar mata da makamai da kuma duk abinda zai da taimaka mata wajen cutar da mutanen kasar. 

Har'ila yau jakadan kasar ta Faransa a majalisar dinkin duniya kara da cewa idan gwamnatin kasar Burundi ta dau matakin ficewa daga wasu kungiyoyin kasa da kasa wannan zai jawo mata zama saniyar ware a duniya. Daga karshe jakadan yayi kira ga kungiyoyin tarayyar Africa Au da kuma ta yankin gabacin Afrika EGAD su kasance masu shiga tsakani a tsakanin ita Burundi da Majalisar dinkin duniya don tabbatar da cewa an dawo da zaman lafiya a kasar ta Burundi.