Batun Kafa Kotu Ta Musamman Kan Rikicin Kasar Jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya
(last modified Fri, 21 Oct 2016 04:07:01 GMT )
Oct 21, 2016 04:07 UTC
  • Batun Kafa Kotu Ta Musamman Kan Rikicin Kasar Jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya

Gwamnatin Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya ta sanar da cewa: Za a kafa kotu ta musamman da zata gudanar da bincike kan matsalolin cin zarafin bil-Adama a kasar tun bayan bullar tashe-tashen hankula a kasar a shekara ta 2003.

Kakakin gwamnatin Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya ya bayyana cewa: A cikin makonni biyu masu zuwa ne za a kai ga sanar da alkalan kotun ta musamman da matsuguninta zai kasance birnin Bangui fadar mulkin kasar domin fara gudanar da ayyukanta musamman gudanar da bincike tare da sauraren koke-koken al'umma kan matsalolin cin zarafin bil-Adama tun daga shekara ta 2003.

A watan Maris na shekara ta 2003 ne gamayyar kungiyoyin 'yan tawayen Seleka suka kifar da gwamnatin Francoin Bozize lamarin da ya janyo bullar yakin basasa a kasar da ya kai ga hasarar rayukan mutane masu yawa tare da tilastawa wasu dubban daruruwa yin gudun hijira.

Majalisar Dinkin Duniya ce zata dauki nauyin dukkanin kudaden da ake bukata wajen tafiyar kotun ta musamman, kuma kotun zata fara gudanar da ayyukanta gadan- gadan ne a farkon shekara mai kamawa ta 2017.