Zaben Nijar 2016 : Mahamadu Isufu Na Kan Gaba
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i1282-zaben_nijar_2016_mahamadu_isufu_na_kan_gaba
Bayanai daga jamhuriya Nijar na cewa saura kiris shugaban kasar mai barin gado Mahamadu Issufu ya lashe zaben tun a zagayen farko kamar yadda yayi alkawari a yakin neman zaben sa.
(last modified 2018-08-22T06:57:52+00:00 )
Feb 25, 2016 14:45 UTC
  • Zaben Nijar 2016 : Mahamadu Isufu Na Kan Gaba

Bayanai daga jamhuriya Nijar na cewa saura kiris shugaban kasar mai barin gado Mahamadu Issufu ya lashe zaben tun a zagayen farko kamar yadda yayi alkawari a yakin neman zaben sa.

kawo yanzu dai a cikin gundumomi 196 cikin 308 da aka bayana sakamakon su dan takara Mahamadu Isufu na jam'iyyar PNDS Tarraya nada kaso 49.44%, yayin da dan takara Hama Amadu na jam'iyyar Moden Lumana dake garkame a gidan kurkuku bisa zargin safara jarirai ke da kaso 16.27%, sai kuma Seyni Omar na jam'iyyar MNSD-Nassara dake da kaso 10.65%.

Sauran masu biye masu sun hada da Mahamane Usman na MNRD Hankuri, sai Ibarhim Yakouba na MPN-Kishin Kasa, cen kuma sai Kassoum Moctar na CPR-Inganci.

'yan adawa dai a wannan kasa sunyi fatali da sakamakon da hukumar zaben kasar CENI ta soma fitarwa a ranar Talata data gabata.

hukumar ta CENI dai nasa ran fitar da sakamakon zaben da aka kada a ranakun Litinin da Lahadi a yau Alhamis.

bisa dokar zabe dai a Nijer duk dan takara daya samu kaso sama da 50%, shi zai lashe zaben, bama sai an je zagaye na biyu ba.