Kotun Daukaka Kara Ta Daure Hambararren Shugaban Masar Morsi Shekaru 20
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i12820-kotun_daukaka_kara_ta_daure_hambararren_shugaban_masar_morsi_shekaru_20
Rahotanni daga kasar Masar sun bayyana cewar wata kotun daukaka kara a kasar ta tabbatar da hukuncin daurin shekaru 20 da aka zartar wa hambararren shugaban kasar Muhammdd Morsi, wanda hakan shi ne farkon hukunci na karshe da aka zartar kan hambarararren shugaban.
(last modified 2018-08-22T06:59:07+00:00 )
Oct 23, 2016 02:54 UTC
  • Kotun Daukaka Kara Ta Daure Hambararren Shugaban Masar Morsi Shekaru 20

Rahotanni daga kasar Masar sun bayyana cewar wata kotun daukaka kara a kasar ta tabbatar da hukuncin daurin shekaru 20 da aka zartar wa hambararren shugaban kasar Muhammdd Morsi, wanda hakan shi ne farkon hukunci na karshe da aka zartar kan hambarararren shugaban.

Rahotannin sun ce kotun daukaka karar ta tabbatar da hukuncin ne kan tsohon shugaban wanda aka hambarar a shekarun baya hukuncin shekaru 20 din saboda hannu da yake da shi a mummunar tarzoma a wajen fadar shugaban kasar a 2013.

Har ila yau rahotannin sun ce  Kotun ta amince da hukuncin da aka zartas a kan wasu na hannun daman hambararren shugaban su takwas.

Tun kawar da gwamnatin tasa dai ake tuhumar shugaba Mursi da wasu mukarrabansa na kungiyarsu ta Muslin Brotherhood.