An kama wani jagoran 'yan tawayen Ruwanda
(last modified Tue, 25 Oct 2016 05:54:45 GMT )
Oct 25, 2016 05:54 UTC
  • An kama wani jagoran 'yan tawayen Ruwanda

Rahotanni daga birnin Goma na Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango na cewa, sojojin kasar sun cafke daya daga cikin shugabannin 'yan tawayen kasar Ruwanda na FDLR da ke yakin gabashin kasar

Da yake magana Menjo Guillaume Ndjike, mai magana da yawun rundunar sojojin kasar ta Kwango ya ce sojojinsu sun kame Kanal Habiarimana Mucebo Sofuni, da ke a matsayin babban kwamanda na farin kaya na Kungiyar ta FDLR aranar  Lahadi da ta gabata a garin Kiwanja.

Daga nata bangare kungiya mai zaman kanta ta Cepadho da ke kula da demokaradiyya da yancin dan Adam mai cibiya a arewacin Kivu ta tabbatar da wannan labari. Garin na Kiwanja dai na a nisan km 75 a arewacin Goma, kuma tuni aka fice da Kanal Mucebo Sofuni din ya zuwa birnin Goma domin yi masa tambayoyi.Kungiyar FDLR dai ta kasance ta 'yan tawayen Hutu na kasar Ruwanda wadda aka kafa bayan kisan kare dangi na 'yan Tutsi da ya wakana a shekara ta 1994 a Rwanda.