Wani sabon rikici ya barke a kasar Afirka ta tsakiya
Akalla Mutane 10 ne suka rasa rayukan su sanadiyar wani sabon rikici da ya barke a kasar Afirka ta tsakiya
Majiyar tsaron Afirka ta tsakiya ta habarta cewa wani sabon rikici ya barke tsakanin kungiyoyi masu dauke da makamai jiya Lahadi a Bangui babban birnin kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar Mutane Akalla guda goma,wannan rikici na zuwa ne a yayin da Ministan tsaron kasar Faransa Jean-Yves Le Drian ya kai ziyara birnin na Bangui a daren jiya Lahadi tare da tabbatar da kawo karshen aikin wanzar da zaman lafiya na Dakarun kasar sa a kasar Afirka ta tsakiyan.
Majiyar ta kara da cewa Ministan Tsaron kasar Faransa ya gana da shugaban kasar Afirka ta tsakiya Faustin-Archange Touadéra da kuma Shugabanin Dakarun wanzar da zaman lafiya a kasar, sannan ya gabatar da jawabi a zauren majalisar Dokokin kasar da misalin karfe 9 na safiyar yau litinin.
Kwanaki biyu kafin ziyarar Ministan tsaron kasar Faransan a tsakiyar Afirkan an yi bata kashi tsakanin kungiyoyin dake dauke da makamai a kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar Mutane akalla 25.
Tun a watan Desambar na shekarar 2013 ne kasar ta Faransa ta aike da Sojoji 2000 zuwa kasar Afirka ta tsakiya sakamon barkewar rikicin kabilanci gami da na addini a kasar.