Tashin Bom A Kasar Buurndi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i1333-tashin_bom_a_kasar_buurndi
Mutane Sun Jikkata Sanadiyyar Tashin Bom A Burundi
(last modified 2018-08-22T06:57:52+00:00 )
Feb 26, 2016 15:33 UTC
  • Tashin Bom A Kasar Buurndi

Mutane Sun Jikkata Sanadiyyar Tashin Bom A Burundi

Kamfanin Dillancin Labarun (AFP) ya nakalto cewa; Mutane shida ne su ka jikkata sanadiyyar fashewar gurneti a yankin Buyenzi da ke babban birnin kasar Buurndi, Bujumbura.

Wani mutum mai suna Freddy Mbonimpa wanda ya ganewa idanunsa abinda ya faru, ya fadawa kamfanin dillancin labarun (AFP) cewa; Daya daga cikin wadanda su ka jikkatan yana cikin mummunan yanayi.

A jiya alhamis ma dai an jefa wasu gurnetin a yankunan Jabe da Musaga da su ke kudancin kasar.

Kasar Burundi ta fada cikin cikin dambaruwar siyasa tun bayan da shugaba Pieer Nkurunziza ya yi tazarce.