Gwamnatin Niger Ta Jaddada Bykatar Yaki Da Yan Ta'adda A Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i13366-gwamnatin_niger_ta_jaddada_bykatar_yaki_da_yan_ta'adda_a_kasar
Gwamnatin kasar Niger ta bayyana cewa yan ta'adda wadanda suke zaune a arewacin kasar Mali sune da alhakin tashe tashen hankula a arewacin kasar a cikin yan kwanakin da suka gabata.
(last modified 2018-08-22T06:59:11+00:00 )
Nov 04, 2016 04:09 UTC
  • Gwamnatin Niger Ta Jaddada Bykatar Yaki Da Yan Ta'adda A Kasar

Gwamnatin kasar Niger ta bayyana cewa yan ta'adda wadanda suke zaune a arewacin kasar Mali sune da alhakin tashe tashen hankula a arewacin kasar a cikin yan kwanakin da suka gabata.

Shafin yanar gizo na Africa Time ya nakalti ministan harkokin wajen kasar Niger Ibrahim Yakuba yana fadar haka a jiya Alhamis ya kuma kara da cewa kasar Niger bada da yan ta'adda a cikin kasar amma yan ta'adda daga arewacin kasar Mali sun addabi arewacin kasar suna kuma tada hankali a sauran kasashen da suke makobtaka da kasar ta Mali,

Yakuba ya kara da cewa a cikin kwanaki goma da suka gabata yan ta'adda daga arewacin kasar Mali sun kai hare hare har sau ukku a arewacin kasar ta Niger, sannan a gefe daya kuma a ranar talatan da ta gabata ne kungiyar Boko Haram suka shigo daga tarayyar Nigeria suka kai wani hare a yankin Difa na kudu maso gabacin kadar.

Daga karshe ministan ya jaddada anniyar gwamnatin kasar na ci gaba da fada da wadannan kungiyyo  na yan ta'adda.