An karfafa matakan tsaro a birnin Alkahirar Masar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i13678-an_karfafa_matakan_tsaro_a_birnin_alkahirar_masar
Kafafen yada labaran kasar Masar sun sanar da karfafa matakan tsaro a birnin Alkahira fadar milkin kasar
(last modified 2018-08-22T06:59:13+00:00 )
Nov 10, 2016 07:20 UTC
  • An karfafa matakan tsaro a birnin Alkahirar Masar

Kafafen yada labaran kasar Masar sun sanar da karfafa matakan tsaro a birnin Alkahira fadar milkin kasar

Kafar watsa labaran Al-Ahad ta kasar Labanon ta habarta cewa a yayin da kungiyoyin siyasa gami da na fararen hula suka kira Al'ummar kasar da su fito a gobe juma'a domin gudanar da zanga-zangar ranar Tallaka,dan nuna adawa da gwamnati kan yadda tattalin arzikin kasar ya lalace, Jami'an tsaron kasar sun karfafa matakan tsaro a birnin Alkahira musamman ma a dandali da gurare masu mahimanci na birnin.

Tun a jiya laraba ne aka jibke jami'an tsaro a dandalin Attahrir da kuma dandalin Tala'at harb, bayan birnin Alkahira an karfafa matakan tsaro a sauren manyan buranan kasar.

A wata sanarwa da kungiyar Talakawan kasar ta fitar jiya Laraba, ta bukaci dukkanin Al'ummar kasar da su fito kwansu da kwalkwatar su domin halartar zanga-zangar da za a gudanar a gobe Juma'a ta nuna adawa da yadda tattalin arzikin kasar ya shiga mawuyacin hali.

Bayan matsalar tsaro, kasar ta Masar na fuskantar matsalar tattalin arziki, barnar dukiyar Gwamnati da rashin kyakkyawan jagoranci , lamarin da ya sanya matsalar rashin aikin yi na matasa ya karu da kashi 40% a kasar.